Gwamnatin jihar Kaduna ta katse layukan sadarwa na wayar salula a wasu kananan hukumomi a jihar domin dakile ayyukan yan ta'adda da yan bindigan daji.
Kwamishinan tsaro na jihar Kaduna Samuel Aruwan, ya bayar da sanarwar haka a Kaduna ranar Laraba 29 ga watan Satumba.
Ya ce Gwamnati ta dauki wannan matakin ne bayan wani taro da ta yi da masu ruwa da tsaki kan sha'anin tsaro na gwamnatim tarayya a jihar Kaduna wanda suka bayar da shawara kan muhimmancin katse layukan sadarwa saboda dalilan ayyukan tsaro.
Rubuta ra ayin ka