Type Here to Get Search Results !

Yan sanda sun bata, an kona mutum da ransa a sabon harin 'yan bindiga a Sokoto


Kwanaki biyu bayan kashe jami'an tsaro a sansanin soji a Sokoto, 'yan bindiga sun sake kai wani sabon hari a jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Sun kai harin ne a karamar hukumar Sabon Birni ta jihar, ranar Laraba 29 ga watan Satumba, inda suka kona wani mutum da ransa kana 'yan sanda suka tsere.

A Sabon Birnin ne 'yan bindigar suka kashe akalla jami'an tsaro 17 a farkon makon nan.

Daily Trust ta tattaro cewa an sace mutane 27, ciki har da mata da yara daga Gatawa, wani gari a Sabo Birni.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, dan majalisar mai wakiltar mazabar Sabon Birni ta Gabas a majalisar dokokin jihar, Sa’idu Ibrahim, ya ce a yanzu haka ‘yan bindigan suna kai hare-hare kan hukumomin tsaro a yankin.

A kalamansa:

“Yanzu suna neman inda jami’an tsaro suke domin sun samu karin karfin gwiwa sakamakon harin da suka kai musu a kwanan baya a wani sansanin soji a Dama inda aka kashe sojoji da yawa, 'yan sanda da jami’an Civil Defence.

“Don haka yanzu suna kai hari a wuraren da suka san akwai sojoji, 'yan sanda ko wani sansanin jami'an tsaro.

“Sun harbe mutane biyu, ciki har da wata mace tare da kona wasu mutane uku da suka buya a cikin kantin hatsi; daya daga cikinsu ya mutu nan take yayin da sauran biyun ke karbar magani a asibiti."

A cewar dan majalisar, sun mamaye Gatawa ne saboda kasancewar sansanin “Operation Puff Adler” a yankin.

“Yayin da nake magana da ku yanzu, har yanzu ba a ga 'yan sanda da yawa ba. Ba mu sani ba ko an sace su ko sun gudu."

Kasurgumin shugaban 'yan bindiga ya tona asirin 'yan uwansa, ya nemi gafara

Goma Samaila, shugaban gungun masu garkuwa da mutane a yankin Rigachukum ta jihar Kaduna, ya bayyana sunayen mambobin kungiyar sa, Daily Trust ta ruwaito.

Mutumin mai shekaru 47, wanda rahotanni ke cewa ya dade yana tafka ta'annuti, ya yi magana kan wasu ayyukansa da adadin kudin da ya karba a matsayin kudin fansa.

A wani faifan bidiyo, an ga Samaila yana rokon gafara yayin da daya daga cikin jami'an tsaron da ya kama shi ke tambayarsa.

Ya roki cewa:

“Ina rokon jinkai da gafara; Ba zan sake aikata irin wannan laifin ba."

Dangane da wasu ayyukan da ya yi, ya ce:

“Mutum na farko da muka yi garkuwa da shi shine Abdul; sun biya kudin fansa N200,000; akan Alhaji Umaru, mun karbi N500,000, Wani kuma Alhaji Birau; sun biya jimillar naira miliyan uku sannan dayan kuma shine Alhaji Ibrahim wanda ya biya N700,000.”

Rahoto: Halin da ake ciki na harin 'yan bindiga duk da katse hanyoyin sadarwa a Zamfara

A wani labarin, alamu sun bayyana cewa har yanzu ana ci gaba da samun kashe-kashe da garkuwa da mutane a jihar Zamfara duk da katse hanyoyin sadarwa a jihar.

Yayin da katsewar da kokarin sojoji ya rage barnar 'yan bindiga tare da kashe su, wasu mazauna jihar sun shaida wa BBC Hausa cewa an ci gaba da kai hare-hare da sace-sacen a jihar.

Don haka, duk da rokon da suke yi wa gwamnatin jihar na tsagaita wuta, kamar yadda Gwamna Bello Matawalle ya bayyana a ranar 10 ga Satumba, 'yan bindigan sun ci gaba da kai hari kan mazauna jihar.

Legit Nigerian


Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies