Da duminsa: Gwamnati ta rufe layukan sadarwa a kananan hukumomi 14 a jihar Sokoto, duba jerin kananan hukumomi


Gwamnatin jihar Sokoto ta rufe layukan sadarwa a kananan hukumomi 14 daga cikin 24 da ke fadin jihar. Shafin isyaku.com ya ruwaito.

Gwamna Aminu Tambuwal ya sanar da haka lokacin wata tattaunawa da sashen Hausa na gidan rediyon VOA ranar Litinin 20 ga watan Satumba.

Wasu daga cikin kananan hukumomi da lamarin ya shafa sun hada da Dange Shuni, Tambuwal, Sabon Birni, Raba, Tureta, Goronyo, Tangaza da karamar hukumar Isa. 

Karamar hukumar Isah tana makwabtaka da karamar hukumar Shinkafi a jihar Zamfara, yayin da kananan hukumomin Goronyo da Sabon Birni suna makwabta da jamhuriyar Nijar, wuraren da matsalar tsaro ya fi kamari sakamakon yawaitan ayyukan yan bindigan daji.

Previous Post Next Post