Abubuwa bakwai da ke sa fatar mutum yin kyau maimakon shafe-shafe


Matan da ke amfani da irin wadanna abubuwa kamar man shafawa ko kuma sabulu sun yarda da cewa abubuwan da suke amfani da su ba su da sinadarai masu karfin lalata jikinsu tun da daga tsirrai aka samo asalinsu.

Abun ban mamaki shi ne duk masu amfani da kayayyakin, fatarsu takan koma a yanayin mutum mai yin shafe-shafe wato fatar tasu ta sauya launi gaba daya ta koma fara. Sai dai inda suka bambanta da masu shafe-shafen, su fatarsu ba ta yin kyalli.

Sannan suna iya shiga cikin rana lafiya kuma jikinsu bai fiya wari ba.

Hakan na nufin cewa wannan 'natural glowing' din ba shi da wani maraba da bilicin kasancewar duka za a iya kiran su da shafe-shafe.

Illolin da wannan shafe-shafen kan iya jawo wa sun hada da cutar daji da ciwon koda da saurin tsufa da lalacewar fata ta daina bayar da kariya ga jiki kamar yadda ya kamata.

Wani kwararren likitan fata a Abuja, Dr Muhammad Bashir Mallan ya bayyana cewa babu bambanci tsakaninsa da bilicin tun da duk aiki daya suke yi, kawai dai sunan yana canzawa da zamani.

"A da ana kiran shafe-shafen da bilicin, a yayin da kan mutane yawaye da illolin da ke tattare da Bilicin mutane suka fara janye jiki, sai aka sauya masa suna daga Bilicin zuwa Toning,

Da kuma aka tona aisirin 'toning' sai ya koma 'Organic' sai kuma ya koma 'Natural Glowing.'

Hakan dai na nufin duka wadannan nau'ikan shafe-shafe ba su da wata maraba duk abu daya ne wato suna ne kawai ake canzawa", In ji Dr Mallan.

Haka zalika, amfani da hadin gida kamar hada wasu daga cikin wadannan lemon tsami da kur-kur da zuma da gahawa da kubewa da kwai da gawayi waje daya bai dace ba a cewar kwararran likitan fata,

"Idan mutum na da wata matsala da fatarsa kamar kuraje ko tabon ciwo ko kaushi da sauransu zai fi dacewa yaje ya samu kwararrun masana a kan fata maimakon ya zauna a gida ya yi hade-hade domin samun waraka."

Abubuwan da mutum zai yi domin samun fata mai lafiya da kyau.

Kwararren likitan, Dr Muhammad Bashir Mallan ya lissafa wasu abubuwa guda bakwai da ya ce idan aka bi su to fatar mutum za ta yi kyau ba tare da yin shafe-shafe ba.

•Shan ruwa mai kyau

•Rage shiga rana

•Cin abinci mai lafiya

•Shan kayan marmari

•A guji amfani da sabulai masu sinadarai masu karfi

•A daina gurza fata da kuma amfani da soso mai kaushi

•Rage yawan damuwa.

Rahotun BBC Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN