Type Here to Get Search Results !

Da duminsa: An cafke 3 daga cikin wadanda suka sace Yan makarantar Bethel Baptist, sun tona wani asiri


Yansanda sun kama mutane uku daga cikin wadanda suka sace fiye da dalibai 100 na makarantar Bethel Baptist da ke Kaduna,

Wadanda aka kama su ne Adamu Bello, Isiaku Lawal da Muazu Abubakar. An kama su sanye da kakin soji.

Kakakin hukumar yansanda na kasa Frank Mba, ya gabatar da su ga manema labarai a Abuja.

Ya ce wadanda aka kama sun amsa laifinsu lokacin amsa tambayoyi wajen yansanda. Ya ce sun gaya wa yansanda cewa sun aikata laifin ne saboda matukar bukatar ganin sun sami kudi.

Daya daga cikin wadanda suka sace yan makarantar mai suna Abubakar dan shekara 27, ya ce:

"Mu 25 muka gudanar da aikin sace yara yan makarantar su 136, kuma mun sami N100,000 kowannen mu daga kudin da muka karba".

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies