Mutane da dama sun mutu sakamakon mumunar hatsarin motar Tirela a garin Ka'oje jihar Kebbi


Mutum biyar yan garin Bagudo a jihar Kebbi sun mutu nan take, wasu mutane da dama sun sami munanan raunuka sakamakon hatsarin motar trela da ya auku da safiyar Alhamis 23 ga watan Satumba.

Majiyarmu ta ce hatsarin ya auku ne bayan gangar jikin motar Trelar ta kwabe daga kan motar, sakamakon haka gangar jikin motar ya fadi ya yi wa jama'a da ke ciki rauni wasu kuma suka mutu.

Kazalika mun samo cewa jama'a da ke cikin motar suna kan hanyarsu ce ta zuwa cin kasuwa a garin Tsamiya eanda ke ci kowane Alhamis. 

Hatsarin ya auku ne a farkon shiga garin Ka'oje.

Wata majiya ta shaida mana cewa mutum 9 da ba a tantance ko yan wani gari bane sun mutu a hatsarin. 


Previous Post Next Post