Birnin kebbi: Kotu ta tura uwa da ta ce danta anabi ne da Mahaifinta zuwa asibiti domin duba lafiyarsu kafin yanke hukunci


Alkalin Kotun shari'a ta 1 da ke Nassarawa a garin Birnin kebbi ta tura Binta Isah da Mahaifinta Aliyu Isah zuwa asibiti domin a duba lafiyarsu kafin Kotu ta yanke masu hukunci bayan mo a zaman Kotu na ranar Alhamis, sun sake nanata ikirarin da suka yi cewa dan da Binta ta haifa Annabi be.

Alƙali Muawiyya Shehu Birnin kebbi, ya bayar da wannan umarni ne a zaman Kotun na ranar 2 ga watan Satumba 2021. Alƙali ya tambayesu cewa ana zarginsu da 


1. Hada Baki domin aikata laifi.

2. Tayar da hankalin jama'a.

3. Cin zarafin Addinin Musulunci.

Ya ce " Mako da ya gabata kun gaya wa Kotu cewa dan Binta mai suna Muhammadu Basiru Annabi ne. Har yanzu kuna kan zancen? Binta da Mahaifinta Aliyu sun ce eh"

Sakamakon haka Alƙali ya bayar da umarni cewa a kai su Asibiti a duba lafiyarsu, sai a dawo da su mako mai zuwa domin yanke hukunci.

Mijin Binta ya ki shiga cikin lamarin

Rahotanni da shafin labarai na isyaku.com ya tattaro, sun yi nuni da cewa Binta mahaifiyar Basiru tana da aure. Sai dai mijinta ya nisanta kansa daga wannan lamari. Mun samo cewa sakamakon haka ya zare hannunsa ya kyaleta da yan uwanta cikin wannan matsala.

Mahaifin Binta Malam Aliyu Isah yana goyon Bayan diyarshi

Aliyu Isah, mahaifi ne ga Binta ba mijinta ba kamar yadda muka sami Labarin farko. Yaro da Binta ta haifa jikanshi ne. Sai dai Aliyu ya dage cewa jikanshi Annabi ne.

Hankalin Binta da Mahaifinta a kwance Babu alamar damuwa tare da su.

A zaman Kotu na ranar Alhamis 2 ga watan Satumba, Binta wacce ke sanye da Hijabi mai klar ja da digo fari gaba daya, tana rike da danta Basiru da ta kira annabi. Yana sanye da rigar dinki jampa mai kala shudi mai duhu.

Mahaifinta Aliyu Isah yana sanye da babbar riga da hulla mai kalar ruwan kasa mai haske. Yanayi da ya bayyana a fuskarsu bai nuna damuwa tattare da su ba a zahiri.

Mai gabatar da kara na yansanda Sgt Faruku Muhammad, mai lambar aiki 493010 ya shigar da kara a madadin Kwamishinan yansandan jihar Kebbi kan Binta da Mahaifinta Aliyu.

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE