Yanzu yanzu: Kotu ta dakatar da shugaban jam'iyar APC na kasa da manbobin kwamitin CECPCKotu ta saukar da Mukaddashin shugaban jam'iyyar APC na kasa Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe daga mukamin shugaban jam'iyyar. Shafin labarai na isyaku.com ya ruwaito.

Kazalika Kotun ta saukar da kwamitin rikon kwarya da Kwamitin tsare tsare  Caretaker/ Extraordinary Convention Planning Committee, CECPC.

Babban Kotun jihar Delta da ke zamanta a Asaba, ranar Laraba 1 ga watan Satumba ta dakatar da Gwamnan tare da wasu jiga jigan jam'iyar daga gabatar da kansu a matsayin shugabanni ko manbobin APC CECPC har sai Kotu ta saurari karar da ke gabanta dangane da lamarin.

Kazalika Alkalin Kotun Justice Onome Marshal Umukoro, da ke sauraron shari'ar, ya dakatar da shirin taron da jam'iyar ke shirin yi ranar 4 ga watan Satumba a jihar.

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN