Da gaske ministan da Shugaba Buhari ya sauke ya yanke jiki ya fadi?


Kwana guda bayan sauke wasu ministoci biyu da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi a ranar Laraba, ake ta yada labarin cewa daya daga cikin ministocin Sale Mamman, ya yanke jiki ya fadi bayan karɓar takardar sallamar.


Kazalika rahotannin da ake yaɗawa na cewa sakamakon hakan an kwantar da saukakken Ministan Ma'aikatar Lantarkin a wani asibiti a Abuja, babban birnin ƙasar.

Jaridun intanet da dama a Najeriyar sun ambato makusantan ministan a matsayin majiyoyin da suka tabbatar musu da labarin.

Amma BBC ta yi nata binciken don gano ko haka lamarin yake ko kuma labarin na ƙanzon kurege ne.

A zantawar da muka yi da Sale Mamman ta wayar tarho, ya bayyana mana yanayin da yake ciki a yanzu.

Tsohon ministan ya ce dama yana fama da rashin lafiya tun a ƙarshen makon da ya gabata.

"Tun kafin a sanar da wannan mataki dama ba ni da lafiya, don ko ofis ban je ba tun farkon makon nan."

Tsohon ministan ya ce dama ya dade ba shi da isasshiyar lafiya don yana yawan zuwa ganin likita ma akai-akai.

"To a jiya Laraba da yau Alhamis ma na koma asibiti don sake duba ni, kuma likita ya ce min ina bukatar hutu don haka na zauna waje guda don na huta," in ji shi.

A yanzu dai tsohon Ministan Lantarkin ya ce ba a kwance yake a asibiti ba kamar yadda ake yadawa, sai dai kuma ba ya gidansa.

"Na samu waje ne mai nutsuwa ina hutawa da shan magani kamar yadda likita ya ba da shawara. Ban zauna a gida ba saboda tururuwar 'yan jaje za ta hana ni hutawar da samun sauki kan kari.

"Amma kuma ba kwantar da ni aka yi a asibiti ba, sannan ban yanke jiki na fadi ba kamar yadda ake ta yadawa."

Wannan layi ne
'Shugaba Buhari ya gode min'
Muhammadu Buhari
Bayanan hoto, Sale Mamman ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya gode masa
Sale Mamman ya kuma ce a ranar Talata da daddare ya gana da Shugaba Buhari ya sanar da shi batun sauke su din, tare da yi masa godiya kan irin gudunmowar da ya bayar a gwamnatinsa.

Ya ce a saninsa ba wai wani laifi ya yi ba da ya sa shugaban ya sauke shi, "dama ko ba a sauke ni yanzu ba dole na sauka nan da shekara biyu," in ji shi.

Sannan ya yi waiwaye kan shekarar 2019 lokacin da aka ba shi minsitan, inda ya ce ba nema ya yi ba, kiransa aka yi aka ce ya tura takardunsa wato (CV), "kuma cikin awa biyu da turawar aka ce an nada ni minista."

Sale Mamman, wanda dan asalin Jihar Taraba da ke arewa maso gabashin Najeriya ne ya ce yana alfahari da irin ayyukan da ya yi a lokacin da yake kan kujerar, musamman sauye-sauyen da ya yi a harkar wutar lantarki a Mambila.

"Kuma ni na raya jam'iyyar APC da ta kusa kai wa kasa a Jihar Taraba," in ji shi.

A karshe ya ce yana da burin ci gaba da harkokin siyasa kuma zai koma siyasa ka'in da na'in.

Rahotun BBC Hausa

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE