Ana zargin wata da kashe ƴaƴan kishiyarta uku a Yobe


Ana zargin wata mata da hallaka yara uku ƴaƴan kishiyarta ta hanyar saka musu guba a cikin shayi.

Wannan lamari ya faru ne a garin Potiskum na jahar Yobe da ke yankin arewa masu gabashin Najeriya.

Mahaifin waɗannan yara Alhaji Haruna da ke zaune a unguwar Makara Huta a Potiskum, ya tabbatar wa BBC da faruwar wannan lamari, inda ya ce yana zargin matarsa da hannu a kisan kuma tuni ƴan sanda suka yi awon gaba da ita.

Yaran dai da ake kyautata zaton sun sha shayin mai guba huɗu ne inda tuni uku daga ciki suka rasu, namiji ɗaya da mata uku, inda ɗayan yaron kuma ke kwance a asibiti inda yake jinya.

Mahaifin yaran ya shaida wa BBC cewa ya ɗauki wannan lamari a matsayin jarabawa inda ya ce kowane bawa da irin jarabtar da ubangiji ke yi masa.

"Wanda ya yi wannan to tsakaninsa da ubangijinsa, ubangijin da ya halicce su, ya fi ni son su, da saninsa da yardarsa aka ɗauki rayukansu.

"Ina wurin aiki aka kirani cewa an ba su shayi kuma ana ganin ciki da wani abu na guba, wanda muka je asibiti muka bincika muka tabbatar hakane," in ji shi.

Alhaji Haruna ya kuma ce ko da aka kai wadda ake zargin gaban ƴan sanda sai ta fake da cewa ba ta da lafiya inda take buƙatar itama a duba lafiyarta.

Daga ɓangaren jami'an tsaro na hukumar 'yan sandan Najeriya, ASP Dungus Abdulkarim, shi ne kakakin ƴan sandan Najeriya a jihar ta Yobe ya kuma tabbatar wa BBC da faruwar lamarin.

ASP Abdulkarim ya bayyana cewa tuni suka kama matar da ake zargi domin bincike kan dalilin da ya sa ta kashe yaran da kuma irin gubar da ta yi amfani.

Ire-iren waɗannan abuuwa na faruwa a arewacin Najeriya inda akasari ake samun mata su cutar da ƴaƴan kishiyoyinsu ko kuma kishiyoyin kansu inda har a wani lokaci suke hallaka su.

Ko a kwanakin baya sai da Rundunar 'yan sandan jihar Neja a Najeriya ta tabbatar da kisan da wata mata ta yi wa kishiyarta mai suna Fatima wacce ba ta cika watanni biyu da aure ba ta kasheta ta hanyar ƙona ta.

Haka ma a kwanakin baya sai da rundunar ƴan sandan Kano ta kama wata mata da ake zargi da kashe ƴaƴanta biyu mace da namiji yan shekara uku da kuma shida, kuma lamarin ya faru ne Unguwar Sagagi Layin 'Yan Rariya a birnin Kano.

BBC Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN