Da duminsa: Yan bindiga sun kashe wani shugaban kungiyar Miyetti Allah bayan neman kudin fansa N20m


Yan bindiga sun kashe Alhaji Abubakar Abdullahi Damba, shugaban kungiyar makiyaya ta kasa ta Miyetti Allah reshen karamar hukumar Lere a jihar Kaduna.

Shugaban, wanda aka fi sani da suna Dambardi, ya ganu da ajalinsa ne a hannun Yan bindigan da asubahin ranar Juma'a 17 ga watan Satumba a kauyensa ta Lere.

Shugaban kungiyar Miyetti Allah na jihar Kaduna Alhaji Haruna Usman Tugga, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce Yan bindigan sun shiga gidan marigayin da karfe 2 na dare kuma suka bukaci ya basu N20m. 

Marigayin ya gaya masu cewa baya da irin wannan kudi, daga bisani ya zagaya da su wajen wasu Yan Fawa da suka hada masa N250,000 cikin wannan daren ya ba Yan bindigan.

Ya ce Yan bindigan basu gamsu da kudin da suka samu ba, sakamakon haka suka tafi da shi kan hanyar Saminaka, Mari, Zango suka kashe shi.

Previous Post Next Post