An yanke wa tsohon shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy shekara daya a gidan yari saboda daukar nauyin tawagar yakin neman zaben sa da bai yi nasara ba. Mr Sarkozy ya sake tsayawa takarar shugabancin kasar a wannan shekarar.
Wata kotu da ke Paris ta kama Mr Sarkozy mai shekara 66 da laifin kashe miliyoyin yuro yayin yakin neman zabensa fiye da yadda doka ta tanada.
Ba a tsara cewa zai yi zaman gidan yari na dogon lokaci ba, amma za a yi masa daurin talala ne a gida a hukuncin da kotun ta yanke.
Ana sa ran zai iya daukaka kara kan hukuncin.
Mr Sarkozy a watan Maris da ya gabata ya kalubalanci wani hukunci da aka yanke masa a wata kara na daban.
Wannan dai shi ne karo na farko da aka tuhumi tsohon shugaban Faransa da laifin cin hanci.
BBC Hausa
Rubuta ra ayin ka