An tube wata mata sumbur aka shafa mata bakin tukunya a fuska aka tilasta ta hau jaki aka zagaya da ita a gari


An tube wata mata mai shekara 45 zindir, aka shafa mata bakin tukunya a fuska kuma aka tilasta ta hawan Jaki bisa umarnin wani malamin addini panchayat a kauyen Thurwal, kilomita 8 daga wajen bauta na Charbhuja a gundumar Rajasthan's Rajsamand a kasar India. Shafin isyaku.com ya ruwaito.

Malamn tsafin ya ayyana wa matar wannan hukunci ne bayan an yi zargin cewa ta kashe yaron yayarta. Dangin ta ne suka yi wannan zargi.

Shugaban yansandan Rajasmand, (SP) Shweta Dhankar ta ce, takaddama ta samo asali ne bayan Vardi Singh ya mutu a wani yanayi mai daure kai. Kuma kauyawan suka yi jana'izarsa ba tare da gaya wa yansanda ba. Sakamakon haka matarshi ta yi zargin cewa kanwar mahaifiyarshi ce ta kashe shi.

Bisa wannan zargi ta tuntubi malamin addini panchayat wanda ya saurari karar a bainar jama'a, bayan sauraron zancen ya ayyana cewa matar da aka yi kara tana da hannu wajen kashe magidancin.

Sakamakon haka kauyawan suka kamata suka tube ta suka shafa mata bakin tukunya a fuska, suka tilasata ta hau jaki suka zagaya da ita a kauyen har tsawon awa daya inji  Dhankar

An kama wadanda suka aikata mata wannan danyen aiki aka tsare su kuma ana ci gaba da gudanar da bincike.
Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari