Ƴan fashin dajin Zamfara sun kai hari Sakkwato


Rahotanni daga Sokoto da ke arewacin Najeriya sun ce wasu mahara da ake zaton ƴan fashin dajin da jami'an tsaro suke yi wa luguden wuta ne a dazukan jihar Zamfara na kwarara cikin wasu yankunan jihar.

Wasu mazauna yankin ƙaramar hukumar Dange-Shuni sun shaida wa BBC cewa maharan sun shiga ƙauyuka da dama na yankin inda suka yi awon gaba da kusan mutum 20.

Gwamnatin jihar Sokoto ta bayyana cewa tun bayan da gwamnatin jihar Zamfara ta fara ɗaukar matakai a kan ƴan fashin dajin, ita ma ta ƙarfafa tsaro a iyakokinta.

Mazauna yankin sun ce cikin kwanaki biyu da suka gabata ƴan bindigar sun kai hare-hare da tsakar dare, inda suka sace mutane da dama a ƙauyukan yankunan Dange-Shuni da Illela.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce ana kyautata zaton cewa ƴan bindigar sun fito daga maƙwabciyar jihar Zamfara ne.

A cewarsa: " 'Yan bindigar sun shiga wani gari da ake kira Fajanbi inda suka yi awon gaba da mutum tara. Maharan sun tafi da mutum guda a wani ƙauye wanda daga bisani ya kubuta, amma bayan dawowarsa mutumin ya ce sun kai su ashirin da 'yan bindigar suka yi garkuwa da su."

A gefe guda, mahukuntan jihar Sokoto sun ce tabbas akwai ƴan fashin daji da kan tsallaka daga jihar Zamfara domin su tafka ta'asa amma ba kamar yadda aka bayyana cewa suna kwasar mutane ba.

Sai dai sun ce tun bayan da gwamnatin jihar Zamfara ta fara ɗaukar matakai a kan ƴan fashin dajin a yankunanta, su ma suka ƙarfafa tsaro a iyakokin jihar.

A cewar Kwamishinan Tsaro na jihar Sokoto, Kanal Garba Moyi, sun ɗauki matakan daƙile ƴan fashin da aka kora daga jihar Zamfara.

Sai dai duk da haka wasu na ganin cewa akwai bukatar ganin cewa gwamnatin jihar Sokoto ta ƙara duba sauran kafofin da mai yiwuwa ta nan ne waɗannan ƴan bindiga da ke tserewa daga jihar ta Zamfara ke shiga Sokoto.

Rahotun BBC

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN