Allah ya yiwa Matar Sheikh Dahiru Usman Bauchi rasuwa, gwamnan Bauchi yayi ta'aziyya


Allah ya yiwa Hajiya Zainab, matar babban Malami, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, rasuwa.

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad AbdulKadir, ya bayyana hakan yayinda ya kai gaisuwar ta'aziyya wa babban Malamin a gidansa.

Gwamna Bala ya kai ziyaran ne ranar Lahadi, 19 ga Satumba 2021.

A cewarsa:

"Ina jimamin mutuwar Hajiya Zainab, matar Sheikh Dahiru Usman Bauchi."

"Jiya na kai gaisuwar ta'aziyya bisa wannan babban rashi. Ba zamu taba manta ire-iren abubuwan da Hajiya Zainab tayi ba."

"A madadin al'umma da gwamnatin jihar Bauchi, ina yiwa Sheikh Dahiru Usman Bauchi da iyalinsa bisa wannan rashi."

Mataimakin Shehu Dahiru Bauchi, Sheikh Umar Sulaiman Ya Rigamu Gidan Gaskiya

Wannan ya biyo bayan mutuwar Sheikh Umar Sulaiman, mataimakin Sheikh Dahiru Bauchi.

Sheikh Sulaiman ya rasu ne ranar Litinin yana da shekara 76 a duniya bayan wata yar gajeruwar rashin lafiya.

Ɗan marigayin, Khadi Mustapha Suleman, wanda ya tabbatar da rasuwar mahaifinsa ga wakilin dailytrust, yace a halin yanzu ana shirye shiryen yi masa jana'iza kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.

Source: Legit

Previous Post Next Post

Information


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari