Type Here to Get Search Results !

Masu garkuwa da 'ya'yanmu na Yawuri sun ce ba kudi suke bukata ba'

I

yayen ɗaliban kwalejin Tarayya ta Yawuri a jihar Kebbin Najeriya, sun koka kan yadda ake ci gaba da tsare da yaransu tsawon sama da wata uku ba tare da sanin wani yunƙurin kuɓutar da su, da hukumomi ke yi ba.

Ƙorafin na zuwa ne lokacin da ɗaliban waɗanda wani mahaifi ya ce adadinsu ya kai 91 ke cika kwana 94 a hannun 'yan fashin dajin da suka sace su.

Tsaka mai wuyar da iyayen yaran suka tsinci kansu na rashin sanin madafa game da halin da yaransu ke ciki ce ta sanya su kara kokawa a wannan lokacin da 'ya'yansu suka share wadannan kwanaki a hannun 'yan bindigar.

Wani daga cikin iyayen ya shaida wa BBC cewa babu wanda ke tuntubarsu daga bangare hukomomi da kuma na wadanda suka yi garkuwa da 'ya'yan nasu.

"Ni ina da 'yata guda da aka a hannun mutanen nan, abin nan ya kai mu makura domin dalilin wannan matsalar gidajenmu sun raunana, domin in baka iya tafiyar da iyali ba za ka yi rikici da iyayensu mata, domin suna cikin matsanaciyar damuwa," in ji wani mahaifi.

"Mun tattauna da gwaman Jihar Kebbi ya ce mana ka da mu damu da wannan matsala za su yi iya kokarinsu domin ganin an kubutar da wadannan yara, cewa ya yi zai zamar masa abin kunya idan bai je ya karbi yaran nan ba, ba za mu ce ba su yin komai ba domin kubutar da su amma ba sa fada mana komai.

"An dauke kwamishina a jihar Neja an karbo shi, yaran Tegina ma an karbo su to mu ba mu san me namu suka yi ba, an manta da su domin babu yaran da manya a cikinsu."

Wani mahaifi shi ma da ya nemi a boye sunansa, ya ce akwai dansa cikin wadanda suke hannun 'yan bindigar.

"Abin da ya jawo wannan matsalar shi ne, wanda ya yi garkuwa da 'ya'yanmu ya ce ba ya bukatar kudi daga wurinmu.

"Dogo bidi sunansa wanda shi ne shugaban dabar da ta dauke 'ya'yanmu" da ya ce yana bukatar wani abu a hannumu da tuni mun sayar da kadaroinmu mun bayar domin kubutar yaranmu, in ji mahaifi na biyu.

Gwamnatin jihar Kebbi tana cewa iyayen tana kokarin ceto su, su kara hakuri

"Kullum ana cewa wai gwamnati na shiri, yaya za a kwashe kusan watanni uku na shiri, wanne irin shiri ne wannan? Da mun tuntube su sai su ce mu yi hakuri mu yi ta a'ddua.

"In kuma mun tuntubi wadanda suka dauki yaran nan sai su ce, musanye suke so a yi tsakanin gwamnati da 'ya'yanmu, muna cikin tsaka mai wuya wallahi."

Tun da farko 'yan makaranta da malamansu 97 aka sace daga kwalejin ta Yawuri amma daga baya aka sako dalibai biyar da malaminsu guda saboda dalilan da aka ce na rashin lafiya kamar yadda rahotanni ke cewa.

Sai dai yayin da wadannan iyaye daga Jihar Kebbi ke kokawa game da wannan lamari, wasu iyayen a Jihar Kaduna ne ke yin farin ciki na sako yaransu da aka yi a karshen mako, wato daliban makarantar Bathel Baptist da aka sace tun a watan Yulin da ya gabata.

BBC ta tattauna da wani mahaifi wanda ya tabbatar da sako yaran da aka yi a ranar Asabar wadanda aka hada su da iyayensu ba tare da bata lokaci ba.

"Tabbas an sako yara 10 a ranar Asabar, amma ni ba a sako yarinyata ba, tun kuma a ranar Asabar din shugaban makarantar Bathel Baptist ya hada yaran da iyayensu, in ji wani mahaifi.

Matsalar tsaro a arewacin Najeriya na kara zama ruwan dare, abin da masu sharhi ke ganin cewa akwai bukatar hukumomi su kara zage damtse domin shawo kanta.

Rahotun BBC Hausa

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies