Abubuwan da suka kamata ku sani game da e-Naira


Babban Bankin Najeriya, CBN, ya ce a watan gobe na Oktoba 'yan kasar za su soma amfani da kuÉ—in intanet na e-Naira.

CBN ya bayyana haka ne a watan sanarwa da ya fitar a wannan makon watanni da dama bayan ya haramta amfani da kudin Cryptocurrency saboda rashin gamsuwa da yadda tsarinsa yake.

e-Naira kudi ne da zai bai wa mutane damar yin harkokin kasuwanci ta intanet.

Ya kara da cewa zai yi aiki da kamfanin fasaha na Bitt Inc., a kokarin fara amfani da kudin intanet na e-Naira.

CBN ya zabi Bitt Inc. daga cikin manyan kamfanonin fasaha da dama da suka fafata wajen ganin sun samu kwangilar aiki tare da Bankin domin samar da wannan kudi cikin tsaro da tsari mai inganci.

Sanarwar da CBN ya fitar ta kuma bayyana wasu daga cikin alfanun kudin na intanet din da suka hada da inganta tsarin kasuwanci, wadatuwar kuÉ—aÉ—e cikin sauki da kuma saukin kasafi da haraji.

Ga wasu abubuwa da suka kamata ku sani game da kuÉ—in intanet na e-Naira:

KuÉ—in na e-Naira zai saukaka kasuwanci cikin sauki amma yana da bambanci da sauran kuÉ—aÉ—en intanet saboda CBN ne kaÉ—ai yake da alhakin samar da shi.

CBN ya ce kuÉ—in na e-Naira zai taimaka wajen gudanar da harkokin kasuwanci cikin sauki da kuma zai kunshi kowa da kowa sannan zai bunkasa tsarin kasuwanci ba tare da amfani da tsabar kuÉ—i ba.

Kazalika tsarin e-Naira ba ya bukatar tsabar kuÉ—i kwata-kwata.

Haka kuma e-Naira ba ya hawa da sauka kamar saura kuÉ—in intanet irin su Bitcoin, sai dai za a rika amfani da shi kamar yadda ake aiki da Naira.

Tun da tsarin e-Naira zai kasance irin na Naira ne, darajarsu za ta zama iri daya da ta Naira.

Tsarin e-Naira zai kasance daban da na yadda ake bude asusu a bankuna; za a samar da wata jaka da za a rika adana kuÉ—in kowanne mutum ta hanyar ba shi wasu lambobi da shi kaÉ—ai ne yake da irin su.

KuÉ—i ne da aka amince kowa ya yi amfani da su a Najeriya, kuma ba zai rika tara kuÉ—in ruwa ba.

Za kuma a samar masa da wasu lambobi na tsaro da za su hana gurbata shi.

BBC Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN