Sauke ministocin da Shugaba Buhari ya yi somin tabi ne - Garba Shehu


Shugaba Muhammadu Buhari ya sauke ministoci biyu na ma'aikatun Noma Sabo Nanono da kuma na Lantarki Sale Mamman.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin shugaban Najeriya, Femi Adesina ya fitar a wannan Larabar bayan taron majalisar koli.

Mista Adesina ya ce Ministan Muhalli, Mohammed Abubakar ne zai maye gurbin Ministan Noma, yayin da karamin Ministan ayyuka, Abubakar Aliyu zai maye gurbin Ministan Lantarki.

Matakin wani É“angare ne na sauye-sauyen da shugaba Buhari ke aiwatarwa, a cewar Femi Adesina.

A shekara ta 2019 Buhari ya fitar da sunayen mutanen biyu cikin waÉ—anda yake son naÉ—awa a matsayin ministoci, kuma majalisa bayan tantacewa ta amince da naÉ—in nasu.

A baya dai Ministan Noma Sabo Nanono ya sha janyo ce-ce-ku-ce tsakanin al'umma musamman lokacin da ya yi batun cewa naira 30 za ta ishi mutum ya ci abinci a Kano.

Somin taɓi

Mai taimaka wa Shugaba Buhari kan yada labarai Malam Garba Shehu a wata hira da BBC ya ce, shugaban da ya naÉ—a su ne ya ga cewa lokacin sauke su ya yi, "saboda haka ya sauke su ya maye gurbinsu da wasu."

Malam Garba Shehu ya ƙara da cewa shugaban ƙasar ya ce wannan saukewar somin taɓi ne, "akwai wadanda za su biyo baya."

"Ya ce wannan taki na farko kenan, da alama wasu na iya biyo baya," in ji shi.

Ya ce hakan na sauke ministocin na nufin sun tafi kenan ba wai wani sabon muƙami za a ba su ba.

"Ba mu sani ba ko nan gaba zai ba su wani muamin, amma a yanzu dai Shugaba Buhari bai ce za su koma wani wajen ba."

Sai dai Malam Shehu ya ce Shugaba Buharin bai bayyana dalilin sauke ministocin ba.

"Shi yake aiki da su, shi yake duba irin yadda suke gudanar da aikinsu ya ce ya gamsu ko bai gamsu ba. Saboda haka shi ne zai iya fadar dalilin da ya sa ya sauke su din.

"Amma mu dai a idanuwanmu ba mu ga wani laifi da suka yi ko aka yi mana bayani akai ba," kamar yadda ya kara da cewa.

BBC Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN