Da duminsa: Yadda wasu yan Majalisar dokoki na jihar Nassarawa su uku suka kure mutuwa, duba dalili


Wasu yan Majalisar dokoki na jihar Nassarawa sun ketare rijiya da baya bayan an buda wa motarsu wuta da bindiga a kan hanyar Awanga da ke jihar Nassarawa. Shafin isyaku.com ya wallafa.


Harin ya auku ne da karfe 10 na safiyar Laraba 1 ga watan Satumba wanda ya rutsa da Hon Samuel Tsebe (APC- Akwanga ta kudu), Hon David Maiyaki (APC- Karu/ Gitata) da Hon Peter Akwanga PDP- Obi 1, suna kan hayarsu ce ta dawowa daga Jana'zar dan uwan Hon Tsebe wanda ya mutu.

Rahotanni sun ce maharan sun fuskanci motar Hon Tsebe ne a lokacin farmakin.

Tsebe ya ce 'Mu uku mun bar garin Akwanga cikin motocin mu, sai dai yayin da muke karasowa kauyen Wowyen  da ke kan hanyar Akwanga/Lafia wanda yake kusa da makarantar koyar da yansandan kwantar da tarzoma MOPOL wajen tsaunukan Ende, yayin da muka nufato wajen gadar kauyen, kawi sai na ji harbi a gefe na. Lamari da ya sa gilashin motar ya fashe.

Tabbas wannn harin an yi shi ne domin a kashe ni".

Kakakin rundunar yansandan jihar Nassarawa ASP Ramhan Nansel, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce yansanda sun kama mutum daya dangane da farmakin kuma suna gudanar da bincike.

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE