Type Here to Get Search Results !

2023: Ina fatan mulki ya cigaba da zama a arewa domin koya wa 'yan kudu darasi, Omokri


Tsohon hadimin shugaban kasa, Reno Omokri ya yi tsokaci a kan yadda gwamnonin arewa suka ce batun mayar wa da ‘yan kudu shugabancin kasa ba ya cikin kundin tsarin mulkin Najeriya.

Omokri ya ce ya ji dadin yadda kungiyar gwamnonin arewa ta ki amincewa da mayar da mulki kudu, kuma ta bar kujerar a arewa don ta koya wa ‘yan kudu karfin hadin kai.

Kamar yadda tsohon hadimin shugaban kasar ya shaida, ‘yan kudu sun taru a zaben 2015 sun hada kai da ‘yan arewa wurin juya wa dan uwan su baya kuma a haka suke tunanin ‘yan arewa za su yarda da su. Ya kara da cewa ai ba a amince wa maha’inci.

Ya fadada bayanin sa inda ya kwatanta yadda tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode ya koma jam’iyyar APC, inda ya ce babu wani dan arewa da zai iya yin hakan.

Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Instagram:

Ina bayan yadda kungiyar gwamnonin arewa ta hana ‘yan kudu amsar mulki. Gara mulki ya ci gaba da tabbata a arewa har bayan 2023 don a koya wa ‘yan kudu karfin hadin kai.

‘Yan kudu sun hada kai sun ci amanar ‘yan uwan su ‘yan kudu a shekarar 2015 kuma a haka suke so ‘yan arewa su yarda da su?

Ko kai za ka yarda da wanda ya ha’inci makwabcin sa da kai? Shi mayaudari ba ya da tabbas. Idan har za su ha’inci wanda ya ke kusa da su, kai kan ka za su iya ha’intar ka. Kalli Femi Fani-Kayode. Babu wani dan arewa da zai iya abinda ya yi! Tabbas!

Legit Hausa

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies