Kebbi@30: Yadda kwarren masani ya koyar da matasa 37 sana'ar dogaro da kai ta amfani da fasahar zamani ba tare da taimakon Gwamnati ba


A cikin watan Satumba jihar Kebbi ta cika shekara 30 da samun jiha. Sai dai wane taimako ne yan asalin jihar Kebbi suka bayar wajen ci gaban jihar Kebbi da jama'arta?.

Malam Isyaku Garba Zuru masani ne kuma kwararre kan ingizon yanar gizo. Kuma dan asalin jihar Kebbi.

Ababen da ya kamata kusa sani

1.Isyaku Garba Zuru ne dan asalin jihar Kebbi na farko da a ya zo da kimiyyar amfani da wayar salula domin shiga yanar gizo a jihar Kebbi tun shekara ta 2006.

2. Shi ne ya fara hadawa tare da fahimtar da jama'a yadda za su amfana da yanar gizo a wayarsu ta hannu, kuma shi ne ke taimakawa yana hada wa jama'a musamman a garin Zuru da Birnin kebbi.

3.Isyaku ya buda wajen sana'ar daidaita matsalar wayar salula ta hanyar amfani da fasahar ingizon zamani, kuma ya koya wa matasa da dama sana'ar ba tare da taimako daga Gwamnati ko wani kamfani mai zaman kansa ba.

4. Isyaku ya koyar da matasa 37 sana'ar amfani da Komputa domin ganowa  tare da gyara matsalar ta hanyar yin amfani da Komputa daga 2008 zuwa 2018.


5. Isyaku ne ya kirkiro tare da assasa kungiyar masu sayarwa da masu gyaran wayar salula, watau Association of handset dealers and technicians. HADTEC, kafin a cusa siyasa da ya wargaza manufa da martabar kungiyar.

6. Isyaku ne mutum na farko da ya fara kirkirowa tare da daukaka sunan jihar Kebbi a shafin yanar gizo na kebbi24 mai zaman kansa.

7. Isyaku ne ya kirkiro shafin labarai na isyaku.com da ya yi fice a arewacin Najeriya har da wasu kasashen Duniya.

8. Shafin isyaku.com na da maziyarta Miliyan 8 kawo yanzu.

9. Isyaku kwarren masani ne wajen amfani da kimiyyar zamani domin yin amfani da yanar gizo a sami kudin halal, hanyar zama madogara ga matasa da yan jihar Kebbi.

Wannan shi ne gudunmuwar Isyaku Garba Ziru wajen ciyar da jihar Kebbi gaba.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN