An tona asirin wadanda suka kashe soji a Sokoto da dabarun da suka bi wajen yi wa sojin lahani


Rundunar Sojin Najeriya ta ce jami'anta 17 sun rasa rayukansu a wani kazamin harin da mayakan ISWAP da taimakon 'yan bindiga masu satar mutane suka kai Sokoto.

Sanarwar da daraktan yaÉ—a labarai na rundunar, Manjo Janar Benjamin Olufemi Sawyerr ya fitar da ke tabbatar da harin na cewa akwai jami'ansu da aka jikkata.

Benjamin Olufemi Sawyerr ya ce gungun maharan sun far musu ne da misalin 5:30 na safiyar Lahadi, bayan samun damar amfani da layin sadarwar Nijar wajen kitsa harin.

Sannan ya kara da cewa 'yan bindiga masu satar mutane sun taimaka musu wajen kai harin a sansaninsu da ke kauyen Burkusuma na karamar hukumar Sabon Birni a Sokoto.

Yankin Sabon Birni na yawaita fuskantar barazanar hare-hare musamman a watanin baya-baya nan daga 'yan bindiga.

Sanarwar ta kuma ce an kashe mayaka da dama da jikkata wasu, ko da yake babu alkaluman da rundunar ta bayar na yawan maharan da aka kashe.

Sannan akwai mayakan da suka tsere zuwa cikin Nijar da yanzu haka ana kan farautarsu a samamen hadin-gwiwa tsakanin sojojin Najeriya da na Nijar, a cewar sanarwar.

Wannan hari na zuwa ne duk da kokarin da mahukunta jihohin arewa maso yamma wajen murkushe mayaka da 'yan bindiga masu satar mutane.

Matsalolin tsaron na daga cikin muhimman dalilai na kaste layukan waya a Zamfara da wasu kananan hukumomi a Sokoto.

'Ana shigar da makamai Najeriya daga kasashe makwabta'

Yanayin da ake ciki na rashin tsaro musamman a yankuna arewacin Najeriya ya kai ga wata babbar jami'ar sojin ruwan kasar ta zargi cewa akasarin haramtattun makaman da ake satar shiga da su kasar na da alaka da jami'an tsaron kasashe makwabta.

Rahotanni sun ambato Kwamado Jamila Abubakar, na yin wannan zargi ne lokacin da ta wakilci Babban Kwamandan sojojin ruwan kasar, Awwal Gambo, yayin wani zaman sauraron jin ra'ayoyin jama'a da kwamitin majalisar kan harkokin tsaron kasa da tattara bayanan sirri ya gudanar.

Shugaban kwamitin harkokin tattara bayanan sirri a majalisar wakilai na Najeriya Sha'aban Ibrahim Sharada ya shaida wa BBC cewa zargin jami'ar bai zo musu da mamaki ba ganin yanayin da tsaron kasar ke ciki.

Sannan ya ce an karbi wannan bahasi kuma za a nazarci da binciker gaskiyar batutuwan da ta gabatar da zarge-zargenta a kai.

Ta dai ce makaman da kasashen da suka ci gaba ke bayarwa gudunmawa ga kasashe makwabtan Najeriya su ne ke ta'azzara matsalolin tsaro a kasar.

Rahotun BBC Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN