Yanzu yanzu: Hatsari ya rutsa da mota Toyota Corolla dauke da fasinja bayan ta shige karkashin motar Trela a garin Alwasa kan titin Argungu


Wani hatsarin mota ya rutsa da wata mota kirar Toyota Corolla da wata babbar mota Trela a kusa da garin Alwada kan titin Argungu zuwa Ambursa ranar Talata 24 ga watan Agusta 2021. Shafin labarai na isyaku.com ya ruwaito.

Lamarin ya faru ne bayan karamar motar Toyota Corolla wacce ke dauke da wasu fasinja ta shige karkashin bayan motar Trela wacce take tsaye a gefen dama a titi yayin da ake sheka ruwan sama da karfe 6:58 na yamma.

Mun samo cewa motar Toyota ta yi lodin fasinja ne zuwa garin Jega daga garin Argungu kafin faruwar lamarin.

A daidai lokacin da wakilinmu ya isa wajen da lamarin ya faru, ya tarar an kwashe fasinja da direban karamar motar zuwa Asibitin garin Argungu.

Babu rahotun rasa rai ko matakin raunuka da ake tsammanin fasinjan sun samu a daidai lokacin rubuta wannan rahotu.
Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE