Tsohon soja mai shekaru 96, ƴaƴa 50 da mata takwas da ke safarar wiwi tsawon shekaru 39 a jihar Niger


Jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA, sun kama wani tsohon soja mai murabus, Pa Joseph Owherhi, a garin Suleja da ke jihar Niger kan safarar miyagun kwayoyi, Daily Trust ta ruwaito.

Kakakin hukumar Femi Babafemi, a ranar Talata a Abuja ya ce an kama tsohon ne a gidansa da ke Rafin Sanyi a Suleja a ranar Asabar, 21 g watan Agusta da kilo giram na wiwi bayan samun bayannan sirri, Vanguard ta ruwaito.

Tsohon ya ce shekarunsa 39 yana safara wiwi

Da aka yi masa tambayoyi, Owherhi, wanda ya amsa cewa laifinsa ya ce ya fara safarar kwayan ne tun lokacin da ya yi murabus daga aikin soja a 1982.

Ya kuma yi ikirarin yana da matan aure 8 da 'ya'ya 50 kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Har wa yau, NDLEA ta kama wasu mutane hudu da ake zargin masu safarar miyagun kwayoyi ne zuwa kasashen ketare yayin da suke yunkurin tsallaka iyakar kasar a kan babur a kauyen Kolere da ke karamar hukumar Mubi zuwa Kamaru a ranar Asabar dauke da Tramadol da ake boye cikin katon din taliya.

Babafemi ya ce wadanda aka kama din sun hada da Umar Mohammed, Ibrahim Aliyu, Aliyu Adamu da Usman Adamu.

A wani labarin daban, Hukumar ‘yan sandan jihar Oyo sun kama wani Adeyemi Tosin, mai shekaru 36, wanda ma’aikacin banki ne bisa zarginsa da kwasar naira miliyan 10 daga asusun wani abokin huldar bankin, Oladele Adida Quadri.

Kakakin hukumar, DSP Adewale Osifeso, ya bayyana hakan a wata takarda a ranar Talata, 17 ga watan Augusta, inda yace Tosin ya saci kudin Quadri, mai shekaru 78 ne da sunan zai taimake shi a reshen bankin na Ibadan bisa matsalar da ya samu wurin cirar kudi a ranar 12 zuwa ranar 13 ga watan Augusta.

Binciken ‘yan sandan ya haifi da mai ido sakamakon umarnin kwamishinan ‘yansandan jihar, Ngozi Onadeko, wacce tasa a yi bincike na musamman.

Source: Legit.ng

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN