Yadda Yan bindiga suka kai hari makarantar koyar da hafsoshin soji NDA suka kashe mutum biyui


Bayanai daga jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya sun nuna cewa wasu 'yan bindiga sun kai hari Makarantar Sojoji ta Nigeria Defence Academy, NDA, da ke birnin Kaduna. BBC Hausa ta wallafa.

Wasu mazauna gidajen da ke NDA sun tabbatar wa BBC Hausa cewa 'yan bindigar sun kashe sojoji biyu sannan suka sace guda daya yayin harin da suka kai ranar Litinin da tsakar dare.

Sanarwar da mai magana da yawun Makarantar Sojojin, Manjo Bashir Muhammad Jajira, ya fitar daga bisani ta tabbatar da kai harin.

Ya ce 'yan bindigar sun shiga bangaren gidaje na Makarantar inda suka kai hari lamarin da ya yi sanadin mutuwar jami'ansu biyu sannan aka sace guda daya.

Amma bai bayyana mutanen da aka kashe ba, da kuma wanda aka sace. Sai dai wasu bayanai da BBC Hausa ta samu sun tabbatar da cewa an kashe "Lt Cdr Wulah da Flt Lt CM Okoronwo" sannan aka sace Manjo Datong.

"Al'ummar NDA da 'yan makarantar horas da sojoji suna cikin koshin lafiya a Makarantar. Muna tabbatar wa jama'a cewa za a kamo wadannan 'yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba nan gaba kadan, sannan a ceto jami'in da aka sace," a cewar Bashir Muhammad Jajira.

Ya kara da cewa hukumomin Makarantar da hadin gwiwar Runduna Ta Daya ta Sojin Kasan Najerriya da Rundunar Horas da Sojin Sam da ma sauran jami'an tsaro da ke Kaduna sun soma bin bayan 'yan bindigar da zummar far musu da kuma ceto mutumin da aka sace.

Masu sharhi kan lamuran tsaro na ganin harin a matsayin wani abin kunya ga sojoji wadanda a baya, duk karfin halin dan bindiga, ba zai daddara ya kai musu hari ba.

Kazalika wasu na ganin harin a matsayin kololuwar tabarbarewar tsaro a Najeriya, wadda take fama da hare-haren 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN