Yansanda sun kama wani dan Fulani da ya boye a gandun daji dauke da bindiga kirar AK47 a jihar kudu


Jami'an rundunar yansandan jihar Ogun sun cafke wani yaro makiyayi mai suna Muhammad dauke da bindiga kirar AK47 bayan ya boye a cikin gandun daji ranar Talata 10 ga watan Agusta.

Bayan babban jami'in dansanda DPO na ofishin Imeko ya sami labari cewa an gano wasu Fulani guda biyu dauke da bindiga kirar AK47 a gandun dajin CAC Oha a garin Iwoye Ketu da ke karamar hukumar Imeko Afon.

Nan take DPO tare da jami'an ofishinsa, da marawar yan banga, maharbada, sauran yan sa kai, suka fuskanci gandun dajin. Bayan yan awowi a na bincike ne sai aka kama Muhammad boye kuma yana rike da bindiga kirar AK47.

Kakakin hukumar yansandan jihara Ogun DSP Abimbola Oyeyemi, ya sanar wa manema labarai tabbacin kama Muhammad bafulace dauke da bindiga kirar AK47. Ya ce Kwamishinan yansandan jihar Ogun CP Edward Awolowo Ajogun, ya bayar da umarnin mayar da binciken Muhammad zuwa sashen bincike na SCIID domin gudanar da binciken kwakwaf.

Ya ce ana zargin cewa Muhammad yana daya daga cikin gungun yan bindiga da ke addabar yankin ta hanyar sace mutane domin karbar kudin fansa.

Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari