Yan fashi da makami sun kashe wani mai Point of sale POS mai suna Kelly Onomor,a birnin Sapele da ke jiharr Delta ranar Talata 10 ga watan Agusta.
Shafin isyaku.com ya samo cewa yan fashin sun kai samame a shagon Kelly mai POS da ke hanyar Ogodo kusa da Makabarta, kuma suka harbe shi da bindiga a kai bayan ya ki ya mika masu Naira miliyan biyu N2m da ke shagonsa domin kasuwancin ranar Talata.
Akwai mabanbantan rahotanni kan yadda lamarin ya faru. Abokan Kelly sun ce an garzaya zuwa Asibiti da Kelly amma aka tabbatar da mutuwarsa.
Rubuta ra ayin ka