A jihar Sokoto mutum 24 Yan gida daya sun mutu bayan sun ci abinci da aka dafa da gishirin kunshin lalle


Hukumomi a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya sun tabbatar da mutuwar mutum 24 bayan sun ci abinci mai guba. Shafin BBC Hausa ya ruwaito.

Kwamishinan Lafiya na jihar Dr Ali Inname, wanda ya tabbatar da labarin a cikin wata sanarwa, ya ce lamarin ya faru ne a ƙauyen Danzanke da ke ƙaramar hukumar Isa.

Ya ce mutanen sun ci abincin ne da aka yi kuskuren amfani da gishirin lalle a madadin gishirin abinci.

"Kuma dukkanin iyalin gidan, abincin ya yi ajalinsu, mata biyu ne kawai ke raye waÉ—anda suka É—anÉ—ana abincin," in ji shi.

Kwamishinan ya ce yanzu haka ana kula da lafiyarsu a asibiti tare da cike da fatan za su rayu.

Ya ce an yi ƙoƙarin ceton ran waɗanda suka ci abincin mai gishirin ƙunshi amma Allah bai nufa ba.

Ya ce yana da matukar mahimmanci ga jama'a su san cewa lamarin da ya faru ana iya magance shi domin ba al'amari ba ne da ke yaɗuwa, saboda yana da matuƙar hatsarin yin kisa, koda kuwa an ba da kyakkyawar kulawar asibiti ga waɗanda abin ya shafa.

Dr Inname ya ce ya kamata wannan ya zama darasi ga al'umma wanda sau biyu kenan hakan na faruwa a bana bayan al'amarin da ya faru a jihar Zamfara.

Abin da ya kamata a kiyaye

A cikin sanarwar da Kwamishinan Lafiya na jihar Sokoto ya ja hankalin jama'a tare da bayar da shawarwari ga hanyoyin kaucewa sake aukuwar wannan mummunan al'amari.

Daga cikin shawarwarin sun haɗa da keɓe kayan abinci daban da kayayyakin da suka shafi aikin gona da shafe-shafe musamman sinadarai.

Ya kuma ce yana da kyau a duba da tabbatar da kayan abinci kafin amfani da su a girki.

Dole ne a keɓe tare da kiyaye abincin da aka dafa da kuma ruwan sha.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN