Rundunar yansandan jihar Osun ta kama wani Lauyan bogi dan shekara 35 mai suna Muhammed Aliyu Agbaje.
Yayin da yake gabatar wa manema labarai, Kwamishinan yansandan jihar Osun, CP Olawale Olokode, ya ce wanda aka kama ya zo wajen yansanda ranar 4 ga watan Agusta, watau Muhammed Aliyu Agbaje ya ce shi Lauya ne da ya zo domin ya kare wani da ake bincike akansa sakamakon tuhumar aikata barazana ga rayuwar dan adam. Ya ce Muhammad ya ce ya zo ne daga ofishin Lauyoyi na Barista Adeleye daga Ibadan.
Ya ce daga bisani yansanda sun bankado cewa Lauyaan bogi ne, kuma yana zaune a Owode Ede a jihar Osun. Ya ce yansanda sun gano wasu kayakin zargi a gidansa lokacin bincike.
Kazalika Kwamishinan ya ce Muhammad ya amsa cewa shin kam Lauyan bogi ne, kam,ar yadda ya gaya wa yansanda masu bincike.