Maigida ya lafta wa matarsa dukar kutufo har da zubar mata da jini a garin Birnin kebbi


Wani magidanci ya yi wa matarsa dan karen duka har da rauni da ya zubar da jini a Unguwar bayan Oando da ke garin Birnin kebbi.S

Shafin isyaku.com ya samo cewa, rigima ce ta barke tsakanin miji da matarsa da misalin karfe 10 na safe ranar Asabar. Sakamakon haka mijin matar ya yi mata laga laga da duka har da raunuka da suka fitar da jini.

Mun samo cewa mijin matar wanda ma'aikacin gwamnati ne a daya daga cikin ma'aikatun da ke Sakatariyar Haliru Abdu, ya sha yi wa matarsa mugun duka, kuma an yi zargin cewa yakan yi barazanar cewa idan ya kasheta ya kashe banza, sai dai ya yi hursuna.

Kazalika wata majiya makusanciya ga iyalin, ya shaida mana cewa ma'auratan sun shafe shekara 20 tare, har da samun albarkar haihuwar yara 7. 

Ya ce ba wannan ne karo na farko da mijin matar yake yi mata duka ba. Kuma ya ce surukanshi na daga masa kafa ne saboda zuriar yara 7 da Allah ya basu.

Mun samo cewa zancen na gaban jami'an tsaro a halin yanzu. 

Previous Post Next Post

Information


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari