'Yan sanda da sojoji sun tsananta sintiri ta kasa da jiragen sama a Zamfara


Yan sandan jihar Zamfara da wasu jami'ai daga hukumomin tsaro da suka hada da sojoji sun tsananta sintirin sama da kasa a yankin Gusau zuwa titin Tsafe zuwa Yankara dake karamar hukumar Tsafe ta jihar. Jaridar legit ta wallafa.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, wannan na kunshe ne a wata takarda da mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu ya fitar a Gusau.

Cikakken bayanin jami'an tsaro

Akwai rahotannin sirri da suka bayyana cewa 'yan bindiga na barazanar kai hari wasu yankunan karamar hukumar Tsafe dake jihar.

Rundunar tare da hadin guiwar wasu hukumomin tsaro ballantana sojojin sun tsananta tsaro a Tsafe da kewaye domin baiwa dukiyoyi da rayuka tsaro,"'yan sandan suka ce.

Ana kira ga jama'a da su kwantar da hankalinsu tare da ci gaba da ayyukan su.

Ana karawa da kira ga jama'ar yankunan da su samar da ingantattun bayanai ga hukumomi na ayyukan 'yan bindigan domin daukar mataki," yace.

Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari