An fara shirin yaki gadan gadan da Taliban a Afhanistan, duba abinda ya faru


Mai magana da yawun mayaƙan da ke adawa da Taliban a yankin Panjshir na Afghanistan ya ce ƙungiyarsu za ta nemi tattaunawa kafin ta shiga yaƙi da Taliban ɗin. Shafin BBC Hausa ya ruwaito.

Ali Nazary na ƙungiyar National Resistance Front of Afghanistan ya faɗa wa BBC cewa dubban mayaƙa sun taru a ƙarƙashin jagorancin Ahmad Massoud, ɗan shahararren mai adawa da Taliban, Ahmad Shah Massoud.

Nazary ya buƙaci Taliban ta shiga tattaunawa ta gaskiya, yana mai cewa mayaƙan Massoud sun shirya shiga yaƙi.

"National Resistance Front of Afghanistan ta aminta cewa idan ana neman zaman lafiya wajibi ne a gano bakin zaren matsalolin Afghanistan," in ji shi.

"Afghanistan ƙasa ce mai al'ummomi daban-daban, tana buƙatar a rarraba iko ta yadda kowa zai samu muƙami."

Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari