Sabuwar dokar mai: Abin da ake hasashen zai faru da Talakawan Najeriya?


Hukumar da ke kula da farashin mai a Najeriya ta bayyana cewa akwai matakai da gwamnati ke ɗauka ta yadda ba za a samu hauhawar farashin mai ba sakamakon sauye-sauyen da sabuwar dokar inganta harkar ta kawo a ƙasar. Shafin BBC Hausa ta ruwaito.

Tun da gwamnatin APC a Najeriya ta sanar da matakin rusa babban kamfanin mai na ƙasar NNPC a cikin sauye-sauyen da za a yi wa fannin man kasar karkashin sabuwar dokar inganta harkokin man fetur, ƴan ƙasar ke bayyana fargaba ga yiyuwar tsadar farashin man fetur.

Babban jami'in hulÉ—a da jama`a na hukumar PPPRA da ke kula da farashin mai a Najeriya Kimchi Apollos, a hirarsa da BBC ya kawar da fargabar da wasu ke yi cewa za a samu karin farashin mai.

Ya ce gwamnati na tattaunawa da ɓangaren ƙungiyoyin kwadago da nufin ɗaukar matakan da za su taimaka wajen ganin farashin man bai jefa ƴan Najeriya cikin wahala ba.

Ya ce tattaunawar É“angarorin biyu ta shafi yadda za a rage tasirin janye tallafi bayan aiwatar da dokar.

Sai dai duk da bai bayyana matakan ba, amma Mista Apollos ya nuna cewa babu tabbas game da farashin domin kasuwa ce za ta daidaita farashin man a Najeriya.

"Idan farashin mai ya ƙara a can Turai to zai iya ƙaruwa, idan kuma ya sauka zai iya sauka a Najeriya," in ji shi.

Wa zai ƙayyade farashi?

Tsadar farashin mai kan yi tasiri ga tashin kayayyakin amfanin yau da kullum.

Akwai sabbin hukumomi da aka samar ƙarƙashin sabon tsarin tafiyar da harakokin mai a Najeriya.

Hukumomin sun haÉ—a da wadda za ta kula da tonon É—anyen mai da kuma hukumar da za ta kula da saye da sayarwa.

Kuma Mista Apollos ya ce aikin PPPRA da ke kula da farashin mai zai koma ƙarƙashin sabuwar hukumar da aikina ya ƙunshi kula da kasuwancin man a Najeriya.

Ya ce hukumar za ta ci gaba da aikinta na sa ido ga farashi - "Hukumar za ta hana ƙarin farashin da ya wuce ƙima da bai kamata ba domin kada a cuci ƴan ƙasa," in ji shi.

Gwamnatin Najeriya dai na cewa sabuwar dokar a PIB za ta kasance mataki na ci gaban harakar mai da gas a Najeriya

Kuma dokar na ƙunshe da tsari da shugabanci da kuma ci gaban al'umomin yankunan da ake haƙo mai da sauran buƙatu da batutuwa da suka shafi harakar mai a Najeriya.

Janye tallafin mai, batu ne da aka daÉ—e yana jan hankali a Najeriya, kasancewar ya shafi dukkanin fannoni na rayuar Æ´an Najeriya.

Gwamnatin APC da ta zo ta ce ba ta da niyyar cire tallafin man, amma daga bisani ta ce dole ta dauki matakin saboda fatan da ake da shi na kwalliya za ta biya kudin sabulu ya gagara samuwa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN