-->

Ads

Yadda wata budurwa ta aika saurayinta barzahu da karfin tuwo saboda ta kama shi da wata masoyiya

Yadda wata budurwa ta aika saurayinta barzahu da karfin tuwo saboda ta kama shi da wata masoyiya


Wata budurwa mai shekara 24 ta halaka saurayinta har ;ahira a kauyen Majeje a Lulekani, da ke daga wajen Phalaborwa, a kasar Afrika ta kudu ranar Asabar. Shafin labarai na isyaku.com ya tattaro.

Juscah Mheleni ta gurfana a gaban Alkalin Kotun Majistare a birnin Lulekani ranar Talata 10 ga watan Agusta bisa tuhumar kisan kai.

Kotu ta garkame ta a Kurkuku har zuwa ranar 13, ga watan Agusta 2021 kafin yansanda su shirya cikakken bayanai da zai kai ga fara bincike kan lamarin.


Mun samo cewa yar kauyen Majeje ta sami labari cewa saurayinta yana tare da wata budurwa a wani wajen shakatawa a wata unguwa da ke kusa. Sakamakon haka ta yi hanzari ta tafi wajen inda ta same shi tare da budurwar suna hira.

Cacan baki ya kaure tsakaninta da saurayinta, daga bisani ta dauko kwalba ta fasa ta caka wa saurayinta mai shekara 36. Sai dai masu agajin gaggawa da suka je wajen don ceton rai bayan an kira su, sun tabbatar da mutuwar saurayin. Daga bisani budurwar ta kai kanta wajen yansanda a garin Namakgale kuma suka kamata.

Kwamishinan yansandan Limpopo Lieutenant General Thembi Hadebeya yi tur da Allah wadai da wannan lamari. Ya shawarci jama'a su kai zukata nesa a yanayi na fushin zargin cin amana da ya jibanci soyayya ko zamantakewa.

0 Response to "Yadda wata budurwa ta aika saurayinta barzahu da karfin tuwo saboda ta kama shi da wata masoyiya"

Post a Comment

Rubuta ra ayin ka

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN