Kotu ta daure wata Daraktar Banki a jihar Arewa tsawon shekara biyar a Kurkuku, duba abin da ta aikata


Alkali M.M. Abubakar na babban Kotun Bauchi ya yanke wa Sarita Aliyu Hello, babban Daraktan Workman Microfinance Bank, Bauchi, hukuncin dauri tsawon shekara biyar a gidan gyara hali bayan ya kamata da laifin aikata ba daidai ba da kudade, da kuma yin aringizon takardu bayan hukumar EFCC ta gurfanar da ita a gaban Kotun.

Shafin isyaku.com ya tattaro cewa, EFCC ta gurfanar da Sarita a gaban Kotun ne bisa zargin cewa a shekarar 2020,  a matsayinta na babban Daraktar Microfinance Bank, ta aikata ba daidai ba da kudi har N4,786,700.00 inda ta yi amfani da lambobin tsaro na sirri na shugaban sashen Bashi na Bankin ta kirkiro sunayen karya  kuma ta kirkiro bukatar bashi na karya, ta amince da bukatar kuma ta biya kanta kudaden.

Ta mincewa da aikata laifin bayan an gabatar mata da hujjojin tuhuma, sakamakon haka Kotu ta yanke mata hukuncin daurin shekara biyar.

Kotu ta umarci Sarita cewa ta biya Bankin adadin kudi N3,786,700 ta hannun EFCC.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN