Na'urar CCTV ta tona asirin wani tsoho da ya saci Kwamputar Laptop ya sa a wandonsa ya yi kokarin ficewa.
Shafin isyaku.com ya ruwaito cewa, a faifen bidiyon an gan yadda wanan tsoho ya ke tsaye a kusa da wannan Laptop, bayan ya duba hagu da dama da gefensa ya kula cewa ba kowa a kusa, sai ya daga rugar Kaftani da yake sanye da ita, ya zazzalo zariyar wandonsa ya dauki Laptop ya saka a cikin wandonsa a gabansa sai ya sake daure zariyar wandonsa ya kuma kama hanyarsa domin ya fita waje.
Kalli bidiyo: