Da duminsa: Yan bindiga sun yi wa Mai gari yankan rago a hari da suka kai wani kauye, duba dalili


Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kai hari Okporo da makwabtanta a karamar hukumar Orlu ta jihar Imo.

Vanguard ta ruwaito cewa harin wanda aka fara a daren Lahadi, 1 ga watan Agusta ya ci gaba har zuwa safiyar Litinin, 2 ga watan Agusta.

Jaridar ta bayyana cewa har yanzu ba a san dalilin kai harin ba, inda ta kara da cewa mazauna garin sun danganta hakan da wasu gungun miyagu masu aikata miyagun laifuka da kuma wasu matsafa wadanda ke yin barna cikin dare.

An kashe shugaban yankin

Sahara Reporters ta bayyana cewa maharan sun kashe wani shugaban yankin wanda ba a bayyana sunan sa ba.

Mazauna sun shiga tashin hankali

Jaridar Vanguard ta ambato wani mazaunin garin yana cewa tashin hankalin "ya yi zafi" saboda mutane ba su yi barci a daren da aka kai harin.

Majiyar ta ce:

"Wadannan masu aikata laifuka suna tafiya cikin walwala cikin dare kuma suna kashewa da lalata komai."

Mazaunin ya yi kira ga gwamnati da ta tura jami’an tsaro zuwa yankunan da ake rikici don kawo karshen hare-haren.

A wani labarin, Rundunar ‘yan sanda a Suleja, Jihar Neja, ta cafke daya daga cikin wadanda ake zargin mai satar mutane ne da ke karbar kudin fansa ta banki a Babban Birnin Tarayya (FCT).

Wannan kenan kamar yadda mai asusun bankin da mai garkuwa da mutanen ya yi amfani da shi, Babawi Abba, ya dauki lauya don ya kare kansa domin ya tabbatar da cewa ba shi da laifi a cikin lamarin.

Daily Trust ta ruwaito cewa mijin daya daga cikin wadanda aka sace, Saheed Adewuyi cewa, ya biya N500,000 a cikin wani asusun bankin Access mai lamba 1403762272 da suna Badawi Abba Enterprise.

Source: Legit

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN