Abin mamaki: Yadda wata budurwa ta rikide ta zama akuya suna tsakar soyayya a dakin saurayi


Wani abin mamaki ya faru a kauyen Mayuge da ke mazabar Navakholo da ke Gundumar Kakamega a kasar Kenya, bayan wani matashi ya ce budurwarsa ta rikide ta zana akuya yayin da suke kwance tare a kan gado.

Joel Namasaka, yana aiki ne a matsayin shamba boy a Soi, ya gaya wa gidan Talabijin na K24TV cewa budurwar ta amince ta zama masoyiyarsa Kamar yadda shafin isyaku.com ya samo, sai dai lamari ya canja bayan sun isa gidansa tare da budurwar. Gidan yana gefen gidan ubangidansa ne a wajen aiki.

ya ce "Komi yana tafiya daidai, sai dai bayan mun shiga dakina tare da budurwar, kawai sai na gan ta rikide ta zama wata babbar akuya da dogayen kahonni".

Shafin isyaku.com ya ruwaito cewa mahaifinsa ya ce na yi mamakin ganin yadda da na ya canja bayan ya dawo daga Kakamega. Daga dawowarsa sai ya fara wasu dabi'u masu ban mamaki.

"Ya fara kone kayakinsa, Yana dukan mutane kuma Yana cire wandon shi da zarar ya gan mace. Kuma ya fara cin abinci a ko da yaushe". Inji mahaifinsa.

Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE