Yadda aka dauke sandar mulki daga ofishin shugaban Majalisar Dokoki na jihar Kebbi a ofishinsa kafin a tsige shi da mataimakinsa


An dami karin haske kan yadda yan Majalisar Dokoki na jihar Kebbi suka tsige shugaban Majalisar Ismaila Abdulmumini Kamba da mataimakinsa Muhammadu Buhari Aliero ranar Talata. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.


Daily trust ta ruwaito cewa wakilinta ya labarta mata cewa an dauke sandar mulki (Mace) daga ofishin shugaban Majalisar ne da sanyin safiyar ranar Talata

Majiyar Daily trust ta ce Yan Majalisar sun aikata haka ne domin su sami damar aiwatar da aniyarsu na cire shugaban Majalisar da mataimakinsa. Ya ce bayan Yan Majalisar sun dauki sandar mulkin, sai suka sami wani waje da har yanzu ba a fadi ko a ina ne ba, suka zauna suka aiwatar da tsige shugabannin.

Sai dai a zauren Majalisar, Magatakardar Majalisar Ahmad Usman Bunza, ya sanar da sunan Dan Majalisar mai wakiltar mazabar Bagudo, Muhammad Abubakar Lolo a matsayin sabon shugaban Majalisar yayin da ya sanar da sunan Muhammad Usman Zuru a matsayin sabon Mataimakin shugaban Majalisar Dokoki na jihar Kebbi.

Dan Majalisa mai wakiltar mazabar Fakai, Lawal Haruna Gele ya gabatar da bukatar tsige Mataimakin shugaban Majalisar Dokoki na jihar Kebbi.

Shugaban kwamitin Majalisar kan harkokin labarai Muhammed Tukur, ya ce uku kadai ne basu sa hannu ba domin cire shugaban Majalisar da mataimakinsa cikin cikin Yan Majalisar 24.

“Twenty-one out of the 24 of us signed for the impeachment. Nobody influenced our decision,” he said. The new speaker and his deputy have since been sworn in.

Contacted, the impeached speaker declined comment, saying “ I won’t talk now.”

Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN