Jarumar Kannywood Umma Shehu ta yi barazanar tona asirin 'yan Hisbah masu neman mata, duba dalili


Hukumar dabbaka koyarwan addinin Musulunci da gyaran tarbiyya watau Hisbah a jihar Kano ta sammaci yar wasar kwaikwayo, Ummah Shehu, zuwa ofishinta. Jaridar legit ta wallafa.

Hisbah ta gayyaci Ummah ne kan zargin da tayi cewa ta san wasu jami'an Hisbah dake neman mata.

BBC Hausa ta ce kwamandan hukumar na jihar Kano, Harun Sani Ibn Sina, ya bayyana mata cewa sun gayyaceta ne don ta gabatar da hujjojin zargin da tayi.

Ibn Sina ya kara da cewa idan bata yi bayani da hujjoji ba, zasu shigar da ita kotu kan laifin yiwa jami'an hukumar kazafi.

Ibn Sina ya ce;

"Ba wai muna nemanta ruwa a jallo ba ne; abin da muke cewa shi ne ta zo ta yi mana karin bayani kan zarge-zargen da ta yi mana domin kowa ya sani.

"Idan abubuwan da ta fada na bukatar bincike za mu bincika, idan kuma ta kasa gamsar da mu, to za mu kai ta kotu domin zargin yi mana kazafi."

Umma Shehu ta yi barazanar tona asirin 'yan Hisbah masu neman mata

Umma Shehu, ta yi barazanar tona asirin jami’an hukumar Hisba ta jihar Kano wadanda ta yi zargin suna neme-nemen mata.

Umma ta bayyana haka ne cikin wani faifan Bidiyo da ya shahara a kafafen sada zumunta, inda take jimamin yadda 'yan Hisbah suka kame wata kawarta, Sadiya Haruna bisa laifin shirya bidiyon batsa.

Wannan na zuwa ne bayan da hukumar Hisbah ta kamewa tare da sanar da gurfanar da wata shahararriya kafafen sada zumunta, wacce aka zarga da yin bidiyon batsa, kuma Hisbah ta ce ya saba doka.

A ikrarin Umma Shehu, Hisbah ba ta da hurumin kame Sadiya Haruna, kasancewar laifi ne wanda idan ma ta aikata tsakanin ta da ubangijinta ne, kuma a cewarta, zai iya yafe mata ya kuma shirye ta.

Source: Legit.ng

Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari