Mawakiya Binta, Jaruma ce yar asalin Masarautar Zuru da ke kudancin jihar Kebbi. Jaruma ce da ke tashe a fagen wakokin harshen Dakarkari ko 'Clela da kuma harshen Hausa. Yar kishin kasa kuma mai son jama'a.
Binta mace ce kamar namiji, bata da raki kuma ga azma da kwarjini a fagen harkokin nishadi, daya daga cikin manyan mawakan jihar Kebbi da ake takama da su, kuma tauraruwar mawakan Masarautar Zuru a halin yanzu.