Da ko jika: Yadda mahaifi ya yi wa diyarsa cikin shege har ta haifa masa jariri


Yan banga sun kama wani mutum mai matsakaitan shekaru mai suna Akpokpokpo bayan ya yi wa diyar cikinsa cikin shege a unguwar Amukpe da ke garin Sapele a jihar Delta.

Sakamakon haka diyarsa mai suna Mercy Akpokpokpo ta haifi jarir mai wata uku da haihuwa a halin yanzu.

Rahotanni sun ce mahaifin yarinyar ya ce zai halaka ta matukar ta rada wa wani zancen. Sai dai bayan fuskantar matsanancin kuncin rayuwa sakamakon haihuwar jariri ba tare da aure ba, yarinyar ta tafi wajen yan banga a unguwar Amukpe kuma ta yi karar mahaifinta ranar Juma'a 27 ga watan Agusta. 

Mahaifin yarinyar ya gaya wa yan banga lokacin da yake amsa tambayoyi cewa sau daya ne ya taba kwana da ita lokaci da yake cikin maye bayan ya sha barasa.

Amma yarinyar ta karyata mahaifinta, ta ce ya kwanta da ita sau hudu ne ba sau daya ba, kuma baya cikin barasa lokacin da yake uwa wajenta domin kwanciya da ita.
Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari