Alkali M.M. Abubakar na babban Kotun Bauchi ya yanke wa Sarita Aliyu Hello, babban Daraktan Workman
Microfinance Bank, Bauchi, hukuncin dauri tsawon shekara biyar a gidan gyara hali bayan ya kamata da laifin aikata ba daidai ba da kudade, da kuma yin aringizon takardu bayan hukumar EFCC ta gurfanar da ita a gaban Kotun.
Shafin isyaku.com ya tattaro cewa, EFCC ta gurfanar da Sarita a gaban Kotun ne bisa zargin cewa a shekarar 2020, a matsayinta na babban Daraktar Microfinance Bank, ta aikata ba daidai ba da kudi har N4,786,700.00 inda ta yi amfani da lambobin tsaro na sirri na shugaban sashen Bashi na Bankin ta kirkiro sunayen karya kuma ta kirkiro bukatar bashi na karya, ta amince da bukatar kuma ta biya kanta kudaden.
Ta mincewa da aikata laifin bayan an gabatar mata da hujjojin tuhuma, sakamakon haka Kotu ta yanke mata hukuncin daurin shekara biyar.
Kotu ta umarci Sarita cewa ta biya Bankin adadin kudi N3,786,700 ta hannun EFCC.