Wutar kendir ta haddasa gagarumar gobara, ta lamushe gidaje 30 a Ribas


Kyandir ya yi dalilin gobarar datayi sanadiyyar kone gidaje fiye da 30 da dukiyoyi masu kimar miliyoyi a wuraren Okwelle dake Mile 2 a Port Harcourt jaridar Legit ta ruwaito. 

Kamar yadda The Nation ta wallafa, an tattara bayanai akan yadda wata mata ta bar kyandir a kunne wanda yayi sanadiyyar wata kazamar gobara wacce tun karfe 6:30 na safe take ci. 

Yaya wannan kazamar gobar ta faru? 


Mun tambayesu ba’asin wutar sai suka ce wata ce ta kunna kyandir tun karfe 6am wutar take ci sai da ko ina ya cinye. Shiyasa kaga duk an taru. Ina nan da yarana muna kokarin ganin mun kashe wutar. 

Sannan mun ga ‘yan kwana-kwana shine muku turasu Okwelle don su kawo dauki. Yanzu haka suna kokarin kashe wutar.

Me ganau suka ce kan gobarar? 


Wani mazaunin yankin, Christain Alali ya ce wutar ta kara ruruwa ne sanadiyyar irin kayan alatun da suke cikin gidajen, The Nation ta ruwaito. A cewarsa: Kasan akwai katako da yawa a wurinnan. 

Kafin masu kashe wuta su iso gaba daya gine-ginen sun kurmushe. Idan ba don masu gadin nan ba da matasa, da kafin masu kashe gobarar su iso komai ya gama lalacewa. 

Wata mazauniya yankin ta bayyana yadda komai nata ya kone kuma ta roka gwamna Nyesom Wike ya tallafa musu.
Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE