Kotu ta dakatar da shugaban jam'iyyar PDP na kasa


Wata babbar kotu a Jihar Ribas da ke kuduncin Najeriya ta dakatar da shugaban jam'iyyar PDP na kasar Uche Secondus. Shafin BBC Hausa ya ruwaito.

Wasu mambobin jam'iyyar biyu ne suka ruga gaban kotun don neman ta hana shugaban na PDP ayyana kansa, a matsayin shugaban jam'iyyar, ko ma jagorantar al'amuranta, bukatun da kotun ta amince da su.

Rikici dai na kara rincabewa a jam'iyyar PDP a baya bayan nan, inda ake ganin akwai gagarumin rashin fahimtar juna tsakanin gwamnan Jihar Rivers Nyesom Wike, da shugaban jam'iyyar PDPn na kasa Uche Secondus.

Ko da a makon jiya sai da dakataccen shugaban jam'iyyar ta PDP ya garzaya wajen tsohon shugaban Najeriya, Chief Olusegun Obasanjo, abun da ake alakantawa da bukatar ganin ya sa baki a takun sakar da ake ganin akwai tsakaninsa da gwamnan Jihar ta Rivers.

A `yan kwanakin nan ma sai da kwamitin amintattun jam`iyyar da sauran jiga-jiganta suka yi wani zama, inda suka takaita wa`adin shugaban jam`iyyar domin a yi babban taronta a watan Oktoba mai zuwa.

''Rikicin na da alaka da 2023''

PDP

ASALIN HOTON, PDP

Tuni masu sharhi suka soma tsokaci a kan dambarwar siyasar cikin gidan da ke ci gaba da girma a jam'iyyar PDP, inda wasu daga cikinsu ke ganin cewa hakan ba ya rasa nasaba da tunkarowar kakar zaben 2023.

Dr Abubakar Kari, masanin siyasa a jami`ar Abuja Najeriya, ya shaida wa BBC cewa kasuwar bukata ce ke tasiri a jam'iyyar ta PDP, don haka kokawa ce ta kaure wadda raba ta sai an yi da gasken-gaske.

A cewarsa ''Akwai sassa daban-daban a jam'iyyar da ke neman su kwace ta, don su biya bukatunsu a zaben 2023, kuma abun mamaki shi Secondus yaron Wike ne, don haka daga nan har zuwa lokacin babban taron jam'iyyar na kasa za a ci gaba da samun wannan tirjiya, kila ma bayan taron ta inda za a zabi shugabanni, inda watakila wasu da zabukan ba su musu dadi ba su nuna kin amincewarsu''

Masanin ya kara da cewa dama haka siyasa ta gada, sannan burin zama wani abu a mulkin siyasa kan haifar a rashin jin dadin idan bai yiwu ba, don haka za a samu wadanda za su ci gaba da yin turjiya.

''Har yanzu PDP tana da karfi kwarai, doon haka wadannan kwararrun 'yan siyasa da suke cikinta su tabbatar da cewa lamarin bai dagule ba, sannan kada su bari masu jawo rikicin su samu galaba'' inji shi

Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE