Abin da ke tsakanina da Ummi Rahab - Adam Zango


Fitaccen tauraron Kannywood Adam A. Zango ya bayyana dalilansa na raba gari da matashiyar jarumar nan wadda shi ya fito da ita idanun duniya, Ummi Rahab.

Yana bayanin ne sakamakon rahotannin da suka karade shafukan sada zumunta da ke nuna yadda dangantaka ta yi tsami a tsakanisu.

A wata hira da BBC, tauraron ya ce duka maganganu da shaci-fadin da ake yi game da abubuwan da suka faru tsakaninsa da matashiyar, wacce ya ce a matsayin 'ya take a wajensa, ba su da tushe ballantana makama.

Amma kuma ya ce yana karbar ko wace irin jarabta da ta zo a gare shi a kan duk wani abu na harkokin rayuwa, don haka ya dauki wannan a matsayin jarrabawar Ubangiji.

"Kowa ya san ni da Ummi, sannan kuma duk mutumin da aka ce ka dauke shi a matsayin ɗa ko 'ya, to sai dai ka yi ta yi masa addu'a a kan hanyar da ya sauya ya kuma bi idan marar kyau ce," in ji shi.

Jaruma Ummi Rahab ba ta ce komi ba kawo yanzu game da kalaman na Zango, amma BBC tana ƙoƙarin samunta domin jin ta bakinta.

Adam ZAngo ya bayyana cewa tun Ummi tana da shekara 11 yake kula da ita, amma ba wai a hannusa take ba, tana gaban iyayenta ne.

"Ina kula da ita ne a cikin masana'antar Kannywood, ina kare ta da kare mata mutuncinta wajen dora ta a kan hanyar da ta dace cikin masana'antar wanda shi ne aikina tun tana da karamin shekaru har zuwa lokacin da ta girma," a cewarsa.

Amma ya ce an datse mata harkar fim din ta tun kafin ta girma, kuma bayan ta girma shi ya sake dawo da ita cikin masana'antar.

Ya ce sun yi hannun-riga ne saboda kauce wa umarnin da ya ba ta na ta rika gudanar da harkokin rayuwarta a bisa hanya madaidaiciya da ya dora ta a kai.

Ya kara da cewa ba wani abu ba ne ya faru tsakaninsa da Ummi in ji Adam Zango, a har mutane suka juye shi ya zama wani abu daban.

"Abubuwa sun faru saboda an ce ka haifi yaro amma ba ka haifi halinsa ba, kuma wanda ka haife shi ma yana iya fin karfinka ballantana wanda ba kai ka haife shi ba ka dauke shi ne a matsyin da, in ji tauraron.

A cewarsa: "Idan dai zan rike yaro in ce masa kada ya yi abu amma ya ce sai ya yi, to an yi kafin ita, kuma da aka zo kan ta ma na ce to ta je Allah ya bayar da sa'a."

''Na yi iya yi na kuma na tabbatar da lokaci zai nuna cewa yadda take a lokacin tana wurina , da kuma yadda ta koma lokacin da bata wurina''.

Zan iya bayar da aurenta

Adam Zango ya kuma musanta maganganun da jama'a ke yi cewa akwai soyayya a tsakaninsa da Ummi Rahab yana mai yana daukarta ne a matsayin 'ya.

Kuma in ji jarumin, duk wadanda ke kusa da shi sun sani, amma kuma wadanda ke nesa suke yi wa abin kallon wani abu daban.

"Soyayya iri-iri ce ai. Akwai soyayya tsakanin mutum da dabba, akwai soyayya tsakanin saurayi da budurwa, akwai tsakanin uba da da, da aboki da aboki, ko kawa da kawa da sauransu, don haka saoyayyar dake tsakanina da Ummi Rahab soyayyar uba da 'ya ne," in ji shi.

Fitaccen jarumin ya kuma kara da cewa shi mai iya zama waliyyinta ne kuma zai iya bayar da aurenta ga duka wanda take so kuma yake son ta.

"Yadda ta ke a matsayin 'ya a wurina zan iya bayar da aurenta ga duk wanda take so, shi wanda ta ke so din watakila da ya biyo hanyar da ta dace zan iya karbar shi hannu biyi in kuma mika ta hannun iyayenta, ya kara cewa".

Amma kuma ya ce yanzu da yake ta riga tabi hanyar da take so babu abin da zai iya yi sai dai kawai ya ce Allah ya bada sa'a.

Labarin takaddama tsakanin fitaccen jarumin Adam A. Zango da 'yar dakin nashi Ummi Rahab dai ta kara zafafa ne bayan da jarumar wallafa wasu kalamai a shafinta na Instagram tana kalubalantar shi da ya daina bata mata suna in ba haka ba allura za ta tono galma.

Rahotun BBC Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN