Yansanda sun kama wasu samari Fulani guda 4 bayan sun aikata wani mugun aiki a jihar Niger


Rundunar yansandan jihar Niger ta kama wasu mutane hudu bisa zargin aikata fashin daji a karamar hukumar Rafi, kuma suka kama su da bindigogi kirar gida a hannunsu. Shafin labarai na isyaku.com ya ruwaito.

Kakakin hukumar yansandan jihar Niger DSP Wasiu Abiodun, ya sanar wa manema labarai ranar Litinin 23 ga watan Agusta cewa an kama su ne a garin Kagara.

Ya ce wadanda aka kama sun hada da Shehu Usman, 21, Idris Ado, 20, Nasiru Dogo a.k.a Badari, 21, da Umar Yahaya,21, dukkansu a sansanin Fulani da ke kusa da kauyen,Garu -gabas a karamar hukumar Rafi ranar 16 ga watan Agusta.

Ya ce wadanda aka kama sun gaya wa yansanda lokacin bincike cewa sun saci shanaye a kauyukan Garun-gabas da Garun-dangana

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN