Ko kun san barci yana kara karfin jima'i, rashinsa na hana haihuwa?


Bacci yana ɗaya daga cikin muhimman buƙatu na ɗan adam a rayuwarsa, kamar yadda masana suka ce idan ba bacci rayuwa ba za ta cika ba.

Hausawa na cewa "dare mahutar bawa" kuma wannan yana da alaƙa da dare da Allah Ya yi domin a yi bacci a huta.

Bacci kamar yadda likitoci suka nuna wani abinci ne da ɗan Adam kan ba jikinsa kuma wata hanya ce ta gina lafiyar kwakwalwa da samun koshin lafiya.

Rashin samun isasshen bacci kan sauya rayuwar mutum, ƙwaƙwalwarsa za ta sauya kuma aikinta zai canza, kamar yadda masana lafiyar ƙwaƙwalwa suka bayyana

Hukumar lafiya ta Birtaniya NHS a wani cikakken bayani da ta yi game da muhimmancin bacci, fa'idarsa da illolinsa ta ce mutum ɗaya cikin uku suna fama da matsalar bacci tare da damuwa da kuma yin aiki ba hutu.

Binciken ya ce bacci yana da muhimmanci ga lafiyar ɗan Adam, domin yana warkarwa da gyara zuciya da jijiyoyin jini. Kuma rashinsa na da alaƙa da hatsarin manyan cututtukan da suka shafi zuciya da ƙoda da hawan jini da ciwon suga da kuma mutuwar jiki.

Sannan dalilan da ke janyo rashin samun isasshen bacci ya fi ƙarfin a ce ɓacin rai ne kawai da kuma rashin mayar da hankali.

Don haka samun isasshen bacci yana da muhimmanci ga ɗorewar rayuwa cikin ƙoshin lafiya da kuma aiwatar da jin ɗadin rayuwar, kamar yadda bincken NHS ya ce bacci na ƙara ƙarfin jima'i da kuma rashinsa na hana haihuwa.

BBC ta tattauna da masanin lafiyar ƙwaƙwalwa, Dr. Shehu Saleh shugaban asibitin masu fama da lalurar taɓin kwakwalwa ta Kware a jihar Sokoto a Najeriya wanda ya yi bayani kan muhimmanci da illolin bacci ga lafiyar ɗan Adam.

Awanni nawa muke buƙatar yin bacci?

Baccin da mutum yake buƙata ya danganta da shekarunsa, domin wasu suna buƙatar da yawa wasu kuma kaɗan ya wadatar da su.

Dr Shehu Saleh ya ce ko wane ɗan adam akwai awannin da ya kamata ya samu isasshen bacci a kullum bisa ga shekarunsa na haihuwa.

Abin da yake da muhimmanci shi ne mutum ya gano adadin baccin da yake buƙata kuma ya yi ƙoƙarin samun baccin domin ƙoshin lafiyarsa.

Masanin ya ce kamar yara ƙanana suna bacci kusan awa 20 a yini daga cikin awa 24 a kullum. Yaran da suka suka tasa suna iya bacci awa 18,

Magidanta da waɗanda suka haura shekara 18 suna buƙatar aƙalla awa 8 domin samun wadataccen bacci.

Wadanda kuma suka haura shekara 60 zuwa 70 , awa shida zuwa hudu ya ishe su, a cewar likitan.

Idan ko wane rukuni na shekaru ya samu wadataccen bacci, zai kasance sun ƙara samun ƙarfi da ƙoshin lafiya a washegari idan ba haka ba, akwai sauyi da matsaloli da yawa da za su fuskanta.

Idan mutum ya tashi daga bacci yana jin kasala kuma daga baya ya ji kamar yana jin bacci, hakan alamu ne da ke nuna mutum bai samu isasshen bacci ba.

Abubuwan da bacci ke ƙarawa

Bacci magani ne ga matsaloli da dama na lafiyar ɗan Adam, kuma likita ya yi bayani game da amfaninsa.

Nasabar rashin bacci ga ƙarfin jima'i da rashin haihuwa

Binciken lafiya ya nuna cewa rashin isasshen bacci yana rage wa maza da mata sha'awar jima'i da kuma rage karfinsa.

Haka kuma an bayyana cewa rashin samun wadataccen bacci na ɗaya daga cikin illolin da ke janyo wahalar samun haihuwa ga maza da mata.

Hukumar lafiya ta Burtaniya NHS ta ce rashin samun wadataccen bacci yana iya zama sanadin rashin haihuwa saboda yadda yake rage ƙwayoyin halitta na haihuwa.

Me zai faru da kai idan ba ka iya bacci

Akwai alamomi da suke faruwa ga ɗan Adam idan bai samu isasshen bacici ba.

Likita ya ce rashin bacci zai shafi dukkanin koshin lafiyar mutum kuma babban hatsari ne ga kamuwa da cututuka da dama.

Dr Shehu Saleh ya bayyana illolin rashin bacci kamar haka:

Shaƙuwa da wayar Salula lokacin bacci

Asalin hoton,

Other

Masana kiwon lafiya sun yi gargaɗi al'umma musamman matasa kan yawan amfani da wayoyin salula a lokacin da ya kamata ace suna bacci.

Masanin lafiyar ƙwaƙwalwa, Dr. Shehu Saleh ya ce rashin samun isasshen bacci na haifar da lalurar kwakwalwa da kuma damuwa.

Masanin ya ce ya kamata mutum ya bambance lokacin bacci da kuma lokacin amfani da wayarsa.

Ya ce shaƙuwa da waya kan haifar da illa sosai ga al'adar mutane ta bacci - kuma matsalar ta shafi yara da manya.

Ba wayar salula muhimmanci lokacin bacci kan janyo wa yara rashin fahimtar karatu da shiga damuwa, a cewar masanin.

Ya kuma ce wani lokaci, rashin bacci kan kasance silar rikicin da ake samu na zamantakewa tsakanin iyali da kuma abokan aiki.

Rama baccin da aka rasa shi ne kawai maganin fatarar bacci.

Idan ka kwashe watanni ba ka samun isasshen bacci, dole ka tsara yadda za ka biya bashin baccin.

Mutum zai iya ƙara awanni a lokacin baccinsa domin rama bashin baccin da yake binsa kansa.

Kamar yadda ake cewa bacci na ƙara yawancin rai, masana sun ce yana da kyau mutum ya ba lafiyarsa muhimmanci ta hanyar gaggauta kwantawa bacci idan lokacinsa ya yi, kuma ya bari har lokacin tashinsa ya yi.

Masana lafiya sun yi gargaɗi kan yawan amfani da magungunan saka bacci domin aikinsu na ɗan lokaci ne kuma za su iya tarwatsa al'adar baccinka.

Rahotun BBC Hausa

Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE