Duba dalili da Gwamna Ganduje ya yafe wa matar da ta kashe mijinta a Kano


Gwamnan Kano da ke arewacin Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi wa wata mata da aka daure a gidan gyaran hali na jihar afuwa bayan samunta da lafin kisan mijinta. BBC Hausa ta ruwaito.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gidajen yarin jihar DSC Musbahu Lawan K/Nasarawa ya aike wa BBC Hausa, Gwamna Ganduje ya bayar da umarnin sakin Rahma Usaini da wasu mutum 30 da ke daure a gidan yarin jihar ta Kano.

Ya ce gwamnan ya dauki matakin ne bayan ganawa da kwamitin shugaban kasa kan rage cinkoson gidajen yari karkashin jagorancin Mai Shari'a Ishaq U. Bello.

Kwamitin ya kuma biya tara ta fursunonin da aka bai wa zabin biyan tara da wadanda suke cikin matsanaciyar rashin lafiya da kuma tsofaffi.

'Kisan mijinta'

An saki Rahma Usaini, mai shekara 20, wacce aka samu da lafin kisan mijinta Tijjani Muhammad a shekarar 2015, bayan ta shekara shida a gidan gyaran hali.

Rahotanni sun ce iyayen Rahma, mai shekara 13 a wancan lokacin, auren dole suka yi mata da Tijjani Muhammad.

A shekarar 2018, alkalin Babbar Kotun Kano, R.A Sadik, ya same ta da laifin kisan kai amma ya ce ba ta balaga ba lokacin da ta aikata laifin.

Daga nan ya ce alhakin gwamnan Kano ne ya yafe mata ko kuma ta ci gaba da zama a gidan yari.

"Bisa shawarwarin jami'an gidan gyaran hali da kuma lura da halayenta masu kyawu, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi amfani da ikonsa na yi wa daurarru gafara inda ya gafarta mata," a cewar DSC Musbahu Lawan K/Nasarawa.

https://www.facebook.com/isyakulabari/videos/1103834420148378/

Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE