Kasurgumin dan bindiga ya gindaya sharrudan zaman lafiya Katsina


Wani fitaccen dan bindiga a jihar Katsina ta arewacin Najeriya ya mika bukatar a biya shi diyyar gidansa da aka kona da matansa da hukumomi suka kama a matsayin sharadin kawo karshen ayyukansa na laifi da yake aikatawa jihar. Shafin RFI Hausa ya ruwaito.

Dan bindigar mai suna Usman Idris mai inkiya da ‘Ruga Kachallah ya kuma bukaci a biya shi hatsinsa da aka salwantar yayin kona gidan nasa.

Wani binciken da jaridar ‘Premium Times’ da ake walafawa a Najeriyar ta gudanar na nuni da cewa Kachalla ne kasurgumin dan bindiga da ya addabi al’umma a yankin karamar hukumar Safana ta Katsina.

Sai dai a cewar jaridar, rundunar ‘yan sandan jihar ta mayar da martani, inda ta ce ba ta bukatar sulhu da Kachalla, duba da cewa ya sha tuba, amma kuma ya koma ruwa bayan dan lokaci.

Majiyoyi sun ce a halin da ake ciki dai Kachalla da yaransa suna cin karensu ba babbaka a yankin na Safana, inda suke daukar mutaneda shanu ba kakkautawa.

Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari